Esther 5:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haman ya fita a ranan da murna, ya kuma ji daɗi. Amma sa’ad da ya ga Mordekai a bakin ƙofar sarki, ya kuma lura cewa bai tashi, ko yă nuna bangirma a gabansa ba, sai ya cika da fushi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ هَامَٰنَ يَڢِتَ دَ ڢَضٍ ثِكِ دَ مُرْنَ سُواْسَيْ؞ دَ يَنَ وُثٜىٰوَ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْ غِدَنْ سَرْكِے، يَكُوَ لُورَ ثٜىٰوَ مُوارْدٜىٰكَيْ بَيْ تَاشِ كُواْ يَنُونَ عَلَمَرْ ڟُواْرُواْ يَايِنْ دَيَكٜىٰ وُثٜىٰوَ بَ، هَامَٰنَ يَثِكَ دَ ڢُشِے سُواْسَيْ غَمٜىٰدَ مُوارْدٜىٰكَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ran nan Haman ya fita da murna da farin ciki, amma da ya ga Mordekai a ƙofar sarki, Mordekai kuwa bai tashi ba, bai kuma yi rawar jiki a gabansa ba, sai ya husata ƙwarai.