Esther 6:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے يَثٜىٰ وَ هَامَٰنَ «كَيِسَوْرِ كَطَوْكِ رِيغُنَنْ دَ دُواْكِنْ، كَتَڢِے وُرِنْ مُوارْدٜىٰكَيْ مُتُمِنْ يَهُودَ وَنْدَ يَكَنْ ذَوْنَ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْ غِدَنْ سَرْكِے، كَيِ مَسَ كَمَرْ يَدَّ كَڢَطَا؞ كَدَ كَضَغٜىٰ كُواْمٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki ya ce wa Haman, “Yi maza, ka ɗauki rigunan da dokin, ka tafi wurin Mordekai, Bayahuden nan, wanda yakan zauna a ƙofar sarki ka yi masa kamar yadda ka faɗa. Kada ka kasa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”