Esther 6:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ هَامَٰنَ يَجٜىٰ يَطَوْكِ رِيغُنَنْ دَ دُواْكِنْ؞ يَسَا وَ مُوارْدٜىٰكَيْ رِيغُنَنْ، يَكُمَسَا مُوارْدٜىٰكَيْ يَهَوْ دُواْكِنْ، سَعَنً يَوُثٜىٰ غَبَنْسَ؞ هَامَٰنَ يَذَاغَيَ دَشِ أَ ڢِيلِ نَثِكِنْ بِرْنِنْ، يَنَ شٜىٰلَ وَمُتَنٜىٰ يَنَ ثٜىٰوَ «دُوبَ أَبِنْدَ عَكٜىٰيِ غَ مُتُمِنْ دَ سَرْكِے يَكٜىٰ مُرْنَ يَغِرْمَمَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haman kuwa ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sa wa Mordekai riguna, ya hawar da shi kan dokin, ya zagaya da shi a dandalin birnin, yana cewa, “Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.”