Esther 6:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki ya ce, “Wa yake a haraba?” Daidai lokacin kuwa Haman ya shigo harabar waje na fada don yă yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a wurin rataye mai laifin da ya shirya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَ ثِكِنْ حَكَ سَيْ هَامَٰنَ يَشِغَ ذَوْرٜىٰ نَوَجٜىٰ نَغِدَنْ سَرْكِے دُواْمِنْ يَيِ مَغَنَ دَ سَرْكِے أَ رَاتَيٜىٰ مُوارْدٜىٰكَيْ عَكَنْ دُواْغُوانْ كَتَكُوانْ رَاتَيَ مُتَنٜىٰنْ دَ يَا رِغَا يَا شِرْيَ؞ سَيْ سَرْكِے يَيِ تَمْبَيَ يَثٜىٰ «وَنٜىٰنٜىٰ أَ ذَوْرٜىٰ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki kuwa ya ce, “Wane ne yake a shirayi?” Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya.