Esther 6:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَبَا طَيَ دَغَ ثِكِنْ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰ مَڢِے غِرْمَ؞ وَنَّنْ بَبَّنْ مُتُمْ كُوَ يَسَا وَمُتُمِنَّنْ دَ سَرْكِے يَكٜىٰ مُرْنَ يَغِرْمَمَ رِيغُنَنْ مُلْكِ؞ يَكُمَ سَاشِ عَكَنْ دُواْكِنْ، يَذَاغَيَ دَشِ أَ ڢِيلِ نَثِكِنْ بِرْنِ، يَيِ تَشٜىٰلَ أَغَبَنْ مُتُمِنَّنْ يَنَ ثٜىٰوَ ‹دُوبَ أَبِنْدَ عَكٜىٰيِ غَ مُتُمِنْ دَ سَرْكِے يَكٜىٰ مُرْنَ يَغِرْمَمَ!› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan a ba ɗaya daga cikin manyan sarakunanka rigunan ya sa wa wanda kake so ka ɗaukaka, ya kuma hawa da shi kan dokin, sa'an nan ya zagaya da shi a dandalin birni, yana shelar a gabansa yana cewa, ‘Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.’ ”