Esther 7:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا أَنْسَيَرْ دَمُو، نِے دَ مُتَنٜىٰنَ، دُواْمِنْ أَ هَلَكَامُ عَكَكَّشٜىٰمُ عَكُمَ كَوَرْ دَمُو؞ دَاعَثٜىٰ أَنْسَيَرْ دَمُو كَوَيْ مُذَمَ بَايِ مَظَا دَ مَاتَادَ نَيِ شِضُ، غَمَا بَابُ كُطِ دَغَ أَبُواْكِنْ غَابَادَ ذَيْ عِيَ بِيَنْ إِرِنْ هَسَرَرْ دَ سَرْكِے ذَيْ يِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba.”