Esther 7:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.” Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ هَرْبُواْنَ، طَيَ دَغَ ثِكِنْ بَابَانِّ مَاسُيِ وَسَرْكِے حِدِمَ يَثٜىٰ «غَاشِ، هَامَٰنَ يَا رِغَا يَا تَادَ دُواْغُوانْ كَتَكُوانْ رَاتَيَ مُتَنٜىٰ مَيْ ڟَيِ وَجٜىٰنْ ڧَڢَا سَبَعِنْ دَ بِيَرْ أَغِدَنْسَ؞ يَتَادَشِ دُواْمِنْ يَرَاتَيٜىٰ مُوارْدٜىٰكَيْ، مُتُمِنْدَ يَثٜىٰثِ رَنْ سَرْكِے؞» سَيْ سَرْكِے يَثٜىٰ «كُرَاتَيٜىٰ هَامَٰنَ عَكَيْ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Harbona, ɗaya daga cikin bābānin da yake yi wa sarki hidima ya ce, “Ga shi ma, Haman ya riga ya shirya gungumen itace a gidansa, mai tsayi kamu hamsin, inda zai rataye Mordekai wanda ya ceci sarki ta wurin maganarsa.” Sai sarki ya ce, “A rataye Haman a gungumen.”