Esther 8:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dokar sarki ta ba wa Yahudawa a kowace birni izini su taru, su kuma kāre kansu, domin su hallaka, su kashe, su kuma hallaka kowace ƙungiyar mayaƙa, na kowace ƙasa, ko lardi, da wataƙila za su kai musu, da matansu, da yaransu hari; su kuma washe mallakar abokan gābansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَوُرِنْ وَطَنَّنْ وَسِيڧُ كُوَ سَرْكِے يَبَا يَهُودَاوَا عَكُواْوَنٜىٰ بِرْنِ إِظْنِ سُتَتَّارَ كَنْسُ دُواْمِنْ سُكَارٜىٰ رَايُكَنْسُ، سُكُمَ هَلَّكَ، سُكَكَّشٜىٰ، سُكَوَرْدَ كُواْوَثٜىٰ أَلْعُمَّرْ دَ ذَاتَ ڢَاطَ مُسُ دَسُو دَ مَاتَنْسُ دَ يَارَنْسُ؞ عَكَ كُمَبَاسُ إِظْنِ سُڨُوثٜىٰ دُكَنْ كَايَنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da 'ya'yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.