Esther 8:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ranar da aka shirya domin Yahudawa su yi wannan a dukan lardunan Sarki Zerzes, ita ce ranar goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato, watan Adar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
رَانَرْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دُواْمِنْ عَيِ وَنَّنْ أَدُكَنْ يَنْكُنَنْ مُلْكٍ سَرْكِے أَهَسُرُسْ عِتَثٜىٰ رَانَ تَغُواْمَشَا عُكُ غَ وَتَنْ غُواْمَشَا بِيُ، وَتُواْ وَتَنْ أَدَرْ كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za a yi wannan a dukan lardunan sarki Ahasurus ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar.