Esther 8:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
’Yan aikan, a kan dawakan fada, suka fita a guje, umarnin sarki yana iza su. Aka kuma ba da dokar a mazaunin masarauta wadda take Shusha.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ یَنْ كَدَتَݣُونَ سُكَ هَوْ دَوَكِنْ سَرْكِے مَاسُ ذَاڢِنْ غُدُ؞ سُكَ ڢِتَ أَغُجٜىٰ، غَمَا دُواْكَرْ سَرْكِے تَنَ ڟَنَنْتَ مُسُ سُيِ سَوْرِ؞ عَكَ كُمَيِ شٜىٰلَرْ وَنَّنْ دُواْكَا وُرِے مَيْ كَتَنْ‌غَ عَبِرْنِنْ شُوشَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai 'yan-kada-ta-kwana suka hau dawakai masu zafin gudu waɗanda akan mora a aikin sarki, suka tafi da gaggawa don su iyar da dokar sarki. Aka yi shelar dokar a Shushan, masarauta.