Esther 8:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu ruwan shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai ruwan shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shusha.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوارْدٜىٰكَيْ كُوَ يَتَاشِ دَغَ غَبَنْ سَرْكِے سَنْيٜىٰ دَ رِيغُنَنْ مُلْكِ مَيْ كَلَرْ ضُوً بُلَ دَ ڢَرِ؞ عَكَ كُمَسَا مَسَ هُولَرْ مُلْكِ مَيْ أَدُوانْ ظِينَارِيَ عَكَنْسَ؞ عَكَسَا مَسَ بَبَّرْ رِغَرْ دَ عَكَيِ دَ لِيلِنْ مَيْݣَوْ مَيْ كَلَرْ جَرْ غَرُورَا؞ دَ يَڢِتَ، سَيْ بِرْنِنْ شُوشَنْ يَأَمْسَ دَ كِرَرِ دَ مُرْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu launin shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai launin shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shushan.