Esther 8:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kowane lardi da kowace birni, ko’ina da dokar sarki ta kai, aka yi farin ciki a cikin Yahudawa, cike da bukukkuwa. Yawan mutane da waɗansu ƙasashe suka zama Yahudawa, don tsoron Yahudawa ya kama su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكُواْوَنٜىٰ يَنْكِ دَ بِرْنِ عِنْدَ عُمَرْنِنْ سَرْكِے دَ دُواْكَرْسَ سُكَ كَيْ، يَهُودَاوَا سُنْثِكَ دَ مُرْنَ دَ ڢَضٍ ثِكِ سُنَيِنْ بِكِ دَ هُوتُ نَمُسَمَّنْ؞ بَنْدَ حَكَمَا، مُتَنٜىٰ دَيَوَ دَغَ ڧَبِيلُنْ ڧَسَرْ سُكَ ذَمَ يَهُودَاوَا، غَمَا ڟُواْرُوانْ يَهُودَاوَا يَكَامَسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kowane lardi da birni inda maganar sarki da dokarsa suka kai, Yahudawa suka yi farin ciki da murna, suka yi biki, suka yi hutu. Mutane da yawa daga cikin mutanen ƙasar suka zama Yahudawa, gama tsoron Yahudawa ya kama su.