Esther 8:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Esta ta sāke roƙon sarki, ta fāɗi a ƙafafunsa tana kuka. Ta roƙe shi yă kawo ƙarshen mugun shirin nan na Haman, mutumin Agag; wanda ya shirya a kan Yahudawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عٜىٰسْتَا تَسَاكٜىٰ ضُواْڧُوانْ سَرْكِے، تَڢَاطِ عَڧَڢَاڢُنْسَ تَنَ كُوكَا؞ تَ ضُواْڧٜىٰشِ يَيِ وَنِ أَبِنْدَ ذَيْ كَوَرْدَ مُغُنْتَارْ هَامَٰنَ مُتُمِنْ أَغَغْ، وَتُواْ شِرِنْدَ يَڧُلَّ وَ يَهُودَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roƙe shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba'agage ya shirya wa Yahudawa.