Esther 9:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta goma sha uku na watan goma sha biyu, wato, watan Adar ne za a aiwatar da dokar da sarki ya umarta. A wannan rana, abokan gāban Yahudawa suka sa zuciya za su sha ƙarfinsu, amma yanzu Zerzes ya canja, Yahudawa kuma suka yi galiba a bisa waɗanda suka ƙi jininsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً أَ رَانَ تَغُواْمَشَا عُكُ غَ وَتَنْ غُواْمَشَا بِيُ، وَتُواْ وَتَنْ أَدَرْ دَيْدَيْ رَانَرْ دَ أَبُواْكَنْ غَابَنْ يَهُودَاوَا سُكَسَا ذُوثِيَا ذَاسُثِكَ عُمَرْنِنْ سَرْكِے دَ دُواْكَرْسَ سُهَلَّكَ يَهُودَاوَا، أَمَيْمَكُوانْ حَكَ سَيْ كُواْمٜىٰ يَثَنْجَ؞ يَهُودَاوَا سُكَ ڢَاطَوَ أَبُواْكَنْ غَابَنْسُ سُكَيِ نَصَرَا عَكَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kan rana ta goma sha uku ga watan sha biyu, wato watan Adar, a ranar da za a aikata maganar sarki da dokarsa, wato a ranar da maƙiyan Yahudawa za su fāɗa musu, sai ranar ta zama ranar da Yahudawa ne za su tasar wa maƙiyansu.