Esther 9:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yahudawa suka tattaru a cikin biranensu a dukan lardunan Sarki Zerzes don su kai wa waɗanda suka nemi a hallaka su hari. Babu wanda ya tasar musu domin mutanen dukan sauran al’ummai sun jin tsoronsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهُودَاوَا سُكَ تَتَّارُ عَبِرَنٜىٰنْسُ أَدُكَنْ يَنْكُنَنْ ڧَسَرْ سَرْكِے أَهَسُرُسْ، دُواْمِنْ سُيِ يَاڧِ دَ دُكْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ دَ نِيَّ سُيِ مُسُ ٻَرْنَ؞ بَابُوَنِ وَنْدَ يَ عِيَ ڢُسْكَنْثٜىٰسُ، غَمَا ڟُواْرُوانْسُ يَڢَاطَوَ دُكَنْ ڧَبِيلُنْ ڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yahudawa suka taru a biranensu a dukan lardunan sarki Ahasurus, don su tasar wa waɗanda suke so su yi musu ɓarna. Ba wanda ya tasar musu gama tsoronsu ya kama mutane.