Esther 9:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ أَوَطَنَّنْ رَانَكُو نٜىٰ يَهُودَاوَا سُكَ هُوتَ دَغَ ڢَطَ دَ أَبُواْكَنْ غَابَنْسُ؞ أَوَنَّنْ وَتَنْ نٜىٰ بَڧِنْ ثِكِنْسُ يَكُواْمَ ڢَضٍ ثِكِ، رَانَرْ كُوكَنْسُ كُمَ تَكُواْمَ رَانَرْ بِكِ؞ عَكَ عُمَرْثٜىٰسُ سُكِيَايٜىٰ رَانَكُنَّنْ سُذَمَ مُسُ رَانَكُنْ بِكِ دَ نَمُرْنَ، رَانَكُو نَعَيْكَ وَجُونَ عَبِنْثِ دَ نَعَيْكَ ݣَوْتَيْ غَ مَتَلَوْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta.