Esther 9:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma sa’ad da sarki ya sami labarin maƙarƙashiyar, sai ya ba da umarnai a rubuce cewa mugun shirin da Haman ya ƙulla a kan Yahudawa yă komo kansa, kuma cewa a rataye shi da ’ya’yansa maza a kan gumagumai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَعَدَّ سَرْكِے يَجِ مُغُنْتَارْ دَ هَامَٰنَ يَشِرْيَ، سَيْ سَرْكِے يَبَادَ عُمَرْنِ أَرُبُوثٜىٰ ثٜىٰوَ دُكْ مُغُنْتَارْ دَ هَامَٰنَ يَشِرْيَ عَكَنْ يَهُودَاوَا يَكُواْمَ كَنْسَ، كُمَ أَ رَاتَيٜىٰشِ دَ یَیَنْسَ مَظَا عَكَنْ دُواْغَيٜىٰنْ كَتَكَنْ رَاتَيَ مُتَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce,cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da 'ya'yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai.