Exodus 1:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
amma Isra’ilawa sun riɓaɓɓanya, suka kuma yi ta haihuwa sosai, suka yi yawan sosai, har ƙasar ta cika da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا ذُرِيَرْ یَیَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ يَلْوَتَ سُكَ حَيْڢِ یَیَ دَيَوَ، سُكَ ڧَارُ حَرْ جَمَعَرْسُ تَيِ ڧَرْڢِے، سُكَ كُمَ ثِكَ ڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.