Exodus 10:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Musa ya miƙa sandansa bisa Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a kan ƙasar dukan dare da kuma dukan yini. Da safe kuwa iskar ta kawo fāra;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُوسَٰى يَمِيڧَ سَنْدَنْ كِيوُانْسَ بِسَ ڧَسَرْ مَصَرْ؞ يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَا سَا إِسْكَرْ غَبَسْ تَيِتَ هُورَاوَ دُكَنْ يِنِ دَ دُكَنْ دَرٜىٰ؞ دَ سَاڢِيَ تَايِ، غَاشِ إِسْكَرْ غَبَسْ تَكَٰوُاْ ڢَارِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar.