Exodus 10:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
suka mamaye ƙasar duka, suka sauka a ko’ina a ƙasar. Ba a taɓa ganin annobar fāra haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin fāra kamar haka ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢَارِنْ كُوَ سُنْذُواْ كُواْعِنَ عَڧَسَرْ مَصَرْ، سُكَ ثِثِّكَ دُكَنْ ڧَسَرْ؞ إِرِنْ وَنَّنْ بَبَّنْ تُلِنْ ڢَارِ، بَعَتَٻَ غَنِنْسَبَ، كُمَ بَذَاعَ سَاكٜىٰ غَنِنْ إِرِنْسَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Farar ta mamaye ƙasar Masar, ta rufe dukan ƙasar. Ba a taɓa ganin fara ta taru da yawa kamar haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin kamar haka ba.