Exodus 10:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka rufe ƙasar har ta zama baƙi. Suka cinye abin da ƙanƙara ta rage, kowane tsiron da yake girma a gonaki, da dukan ’ya’yan itatuwa. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢَرَنْ سُكَ رُڢٜىٰ ڢُسْكَرْ ڧَسَا غَبَاطَيَ، حَرْ ڧَسَرْ تَذَمَ بَڧِ سَبُواْدَ يَوَنْسُ؞ سُكَ ثِنْيٜىٰ دُكَنْ ڟِرٜىٰ ڟِرٜىٰ دَ دُكَنْ یَیَنْ إِتَاثٜىٰنْ دَ سُكَ رَغُ بَايَنْ ٻَرْنَرْ ڧَنْڧَرَ؞ بَابُ طَنْيٜىٰنْ غَنْيٜىٰنْدَ يَرَغُ، كُواْ نَ إِتَاثٜىٰ كُواْ نَڟِرٜىٰ ڟِرٜىٰنْ ڢِيلَيٜىٰ أَدُكَنْ ڧَسَرْ مَصَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ta rufe dukan fuskar ƙasa har ƙasar ta yi duhu. Ta cinye kowane tsiro na ƙasar da dukan 'ya'yan itatuwa waɗanda ƙanƙara ta rage. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.