Exodus 10:28 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Fir’auna ya ce wa Musa, “Fita, ka ba ni wuri! Ka mai da hankali, kada ka ƙara bayyana a gabana, gama ran da ka sāke ganin fuskata, a ran nan za ka mutu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرْعَوْنَ يَثٜىٰ وَ مُوسَٰى «كَڢِتَ دَغَ نَنْ! كَمَيْدَ حَنْكَلِ، كَدَ كَيَرْدَ إِنْ سَاكٜىٰ غَنِنْكَ! ضَنْدَا نَسَاكٜىٰ غَنِنْكَ تُواْ، لَلَّيْ ذَاكَ مُتُ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Fir'auna ma ya ce wa Musa, “Tafi, ka ba ni wuri, ka mai da hankali fa, kada in ƙara ganinka, gama ran da na sāke ganinka ran nan kā mutu.”