Exodus 11:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَثٜىٰ وَ مُوسَٰى «حَرْ يَنْذُ دَيْ، ذَنْعَيْكَ دَ وَنِ بَلَعِ كُمَ عَكَنْ ڢِرْعَوْنَ دَ مَصَرْ؞ بَايَنْ حَكَ ذَيْ بَرْكُ كُتَڢِے؞ عِ، سَعَدَّ يَبَرْكُ كُتَڢِے، ذَيْ كُواْرٜىٰكُ غَبَاطَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yanzu dai zan ƙara bugun Fir'auna da Masarawa sau ɗayan nan kawai da annoba. Bayan wannan zai sake ku. Sa'ad da ya bar ku ku tafi, zai iza ƙyeyarku.