Exodus 12:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti. A rana ta fari, za ku fid da yisti daga gidajenku gama duk wanda ya ci abu mai yisti daga rana ta fari har zuwa rana ta bakwai, za a fid da shi daga Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ «ذَاكُيِ ݣُونَ بَݣَويْ كُنَ ثِنْ غُرَاسَرْ مَرَرْ يِسْتِ؞ أَ رَانَ تَڢَرْكُواْ ذَاكُ كَوَرْدَ يِسْتِ دَغَ غِدَاجٜىٰنْكُ؞ غَمَا دُكْ وَنْدَ يَثِ غُرَاسَ مَيْيِسْتِ تُنْدَغَ رَانَ تَڢَرْكُواْ تَبِكٍ حَرْ ذُوَا رَانَ تَبَݣَويْ، ذَاعَ كَوَرْ دَشِ دَغَ ثِكِنْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra'ila.