Exodus 12:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا يَهْوٜىٰهْ ذَيْبِے تَثِكِنْ ڧَسَرْ دُواْمِنْ يَكَكَّشٜىٰ مَصَرَاوَا؞ عَمَّا سَعَدَّ يَغَ جِنِنْ عَكَنْ سَمَنْ كَتَكُوانْ ڢِرَمْ دَ غٜىٰڢٜىٰ غٜىٰڢٜىٰنْ ڧُواْڢَرْ، يَهْوٜىٰهْ ذَيْ ڧٜىٰتَرٜىٰ وَنَّنْ ڧُواْڢَ، كُمَ بَذَيْ بَرْ مَيْ هَلَّكَرْوَ يَشِغَ غِدَاجٜىٰنْكُ يَكَكَّشٜىٰ یَیَنْ ڢَارِنْكُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa'ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba.