Exodus 12:34 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mutanen suka ɗauki garin da sun kwaɓa ba yisti a ciki, tare da ƙwaryansu na aikin kwaɓan, suka nannaɗe su a mayafansu, suka rataye a kafaɗunsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ طَوْكِ غَارِنْ دَ عَكَ ݣُوٻَ دَ ضُوَ سُكَسَا عَݣُونُواْ، عَمَّا بَسُسَا يِسْتِ عَثِكِيبَ؞ سُكَ نَطَ ݣُونُواْنِنْ ثِكِنْ رِيغُنَنْسُ، سُكَ كُوَ رَاتَيَ عَكَڢَطُنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai jama'ar suka ɗauki ƙullun da ba a sa masa yisti ba, da ƙorensu na aikin ƙullun, suka ƙunshe a mayafansu, suka saɓa a kafaɗunsu.