Exodus 12:36 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji kuwa ya sa Isra’ilawa suka yi farin jini a wurin Masarawa, Masarawa kuma suka saki hannu wa mutanen, suka ba su duk abin da suka roƙa; ta haka Isra’ilawa suka washe Masarawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَسَا إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَ سَامِ ڢَضٍ جِنِ أَعِدَانُنْ مَصَرَاوَا؞ سَبُواْدَ حَكَ مَصَرَاوَا سُكَ بَاسُ دُكْ أَبِنْدَ سُكَ ضُواْڧَا؞ تَهَكَنٜىٰ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَ ݣُوشِ أَرْزِڧِنْ مَصَرَاوَا سُكَ تَڢِے دَشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya sa jama'a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.