Exodus 12:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In akwai wani gidan da ba za su iya cinye rago guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki rago guda gwargwadon yawansu, bisa ga abin da mutum guda zai ci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ أَݣَويْ وَنِ عِيَلِنْ دَ بَذَيْ عِيَ ثِنْيٜىٰ دَبَّ طَيَ طُنْ‌غُمْ بَ، سَبُواْدَ بَسُيِيَوَ أَ عِيَلِنْبَ، تُواْ، سَيْ سُهَطَكَيْ تَرٜىٰدَ وَنِ عِيَلِنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ كُرْكُسَ؞ ذَاعَ رَبَ دَبَّ بِسَغَ يَوَنْ مُتَنٜىٰنْ دَ ذَاسُثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan da wanda iyalinsa ba za su iya cinye dabba guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki dabba guda gwargwadon yawansu.