Exodus 13:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ ڢِرْعَوْنَ يَيِ كُنّٜىٰنْ ڧَشِ يَڧِ يَبَرْمُ مُتَڢِے، سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَكَكَّشٜىٰ دُكَنْ یَیَنْ ڢَارِ مَظَا عَثِكِنْ ڧَسَرْ مَصَرْ دَغَ طَنْ ڢَارِ نَمُتُمْ ذُوَا طَنْ ڢَارِ نَدَبَّ؞ شِے يَسَا كُواْوَنٜىٰ طَنْ ڢَارِ نَدَبُّواْبِے، نَكَنْ مِيڧَشِ هَدَايَ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞ عَمَّا كُواْوَنٜىٰ طَنْ ڢَارِ نَیَیَنَ، نَكَنْ ڢَنْشٜىٰشِ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama sa'ad da Fir'auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan 'ya'yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da 'ya'yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan 'ya'yan farinmu, maza.’