Exodus 14:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Fir’auna ya yi kusa, Isra’ilawa suka ɗaga idanu sai suka hange Masarawa daga nesa suna tā da ƙura suna zuwa. Sai suka tsorata ƙwarai, suka kuwa yi kuka ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَ طَغَ عِدَنُونْسُ سُكَ حَنْغِ ڢِرْعَوْنَ دَ سُواْجُواْجِنْسَ سُنَ ذُوَا وُرِنْسُ، سَيْ سُكَيِ ضَوَرْ جِكِے دُواْمِنْ ڟُواْرُواْ، سُكَيِ كُوكَا غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Fir'auna ya matso, Isra'ilawa kuwa suka ɗaga idanunsu suka ga Masarawa tafe, sun tasar musu, sai suka firgita ƙwarai, suka yi kuka ga Ubangiji.