Exodus 14:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan taurare zukatan Masarawa su shiga don su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir’auna da rundunansa, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے كُوَ ذَنْ تَوْرَرَ ظُكَاتَنْ مَصَرَاوَا دُواْمِنْ سُبِے إِسْرَٰٓءِيلَاوَا حَرْ ثِكِنْ تٜىٰكُنْ؞ نَصَرَاتَ كُمَ عَكَنْ سَرْكِے ڢِرْعَوْنَ دَ دُكَنْ ڧُنْ‌غِيَرْ سُواْجُواْجِنْسَ دَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْسَ دَ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِنْسَ ذَاتَ كَٰوُاْ مِنِ طَوْكَكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir'auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa.