Exodus 14:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da asubahin fāri, sai Ubangiji ya dubi ƙasa a kan sojojin Masarawa daga al’amudin wuta da kuma girgije, sai ya sa suka ruɗe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سَسَّڢٜىٰ كَاڢِنْ وَايٜىٰوَرْ غَرِ، يَهْوٜىٰهْ يَا كَلِّ سُواْجُواْجِنْ مَصَرْ دَغَ ثِكِنْ ڧُنْشِنْ غِرْغِجٜىٰنْ وُتَا، سَيْ يَسَا سُكَ ضِكِثِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da asubahin fāri, Ubangiji, daga cikin al'amudin wuta da na girgije, ya duba rundunar Masarawa, ya gigitar da su.