Exodus 14:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ruwan ya komo ya rufe keken yaƙin da mahayan, dukan sojojin Fir’aunan da suka bi bayan Isra’ilawa cikin teku, ba ko ɗaya da ya tsira.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ضُوً تٜىٰكُنْ كُوَ يَا كُواْمَ يَا رُڢٜىٰ دُكَنْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ ڢِرْعَوْنَ دَ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِنْسَ دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْسَ وَطَنْدَ سُكَبِے إِسْرَٰٓءِيلَاوَا ذُوَا ثِكِنْ تٜىٰكُنْ؞ بَ كُواْ طَيَنْ دَ يَرَغُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ruwan ya komo ya rufe dukan karusai, da mahayan dawakai, da dukan rundunar Fir'auna waɗanda suka bi ta cikin bahar, ba ko ɗaya da ya ragu.