Exodus 14:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَصَرَاوَا سُكَبِے إِسْرَٰٓءِيلَاوَا دَ دُكَنْ دَوَكِنْ ڢِرْعَوْنَ دَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْسَ دَ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِنْسَ دَ كُمَ ڧُنْ‌غِيَرْ سُواْجُواْجِنْسَ؞ مَصَرَاوَا سُكَ سَامِ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا عِنْدَ سُكَيِ ذَنْ‌غُواْ عَبَاكِنْ تٜىٰكُ كُسَدَ غَرِنْ ڢِ هَهِرُواتْ أَغَبَنْ غَرِنْ بَعَلْ ظٜىٰڢُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Masarawa kuwa, da dukan dawakan Fir'auna, da karusai, da mahayan dawakansa, da askarawansa, suka bi su, suka ci musu a inda suka yi zango a bakin bahar, kusa da Fi-hahirot wanda ya fuskanci Ba'alzefon.