Exodus 15:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ دَوَكِنْ ڢِرْعَوْنَ دَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْسَ دَ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِنْسَ سُكَ شِغَ ثِكِنْ تٜىٰكُنْ، يَهْوٜىٰهْ يَا كُواْمَرْدَ ضُوَ عَكَنْسُ، ضُوً كُوَ يَا رُڢٜىٰسُ كَكَڢْ؞ عَمَّا إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَبِے تَثِكِنْ ڟَكِيَرْ تٜىٰكُنْ عَكَنْ بُوسَشِّيَرْ ڧَسَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama sa'ad da dawakan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa suka shiga bahar, Ubangiji ya komar da ruwan bahar a bisansu, amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busassiyar ƙasa ta tsakiyar bahar.