Exodus 15:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوسَٰى كُوَ يَبِدَ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَغَ تٜىٰكُنْ ثِيَوَرْ إِوَ، سُكَ شِغَ ثِكِنْ دَاجِنْ شُرْ؞ سُكَيِ تَڢِيَ عَثِكِنْ وَنَّنْ دَاجِ ݣُونَ عُكُ، بَسُ سَامِ ضُوَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Musa kuwa ya bi da Isra'ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba.