Exodus 17:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma mutanen suka yi fama da ƙishirwa a can, suka yi gunaguni a kan Musa. Suka ce, “Don me ka fitar da mu daga Masar, ka sa mu da ’ya’yanmu da dabbobinmu, mu mutu da ƙishirwa?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا جَمَعَ سُنَ ڢَامَ دَ ڧِشِنْ ضُوَ سُواْسَيْ، سُكَ ثِيغَبَدَ غُنَغُنِ عَكَنْ مُوسَٰى سُكَثٜىٰ «دُوانْمٜىٰ كَڢِتَرْ دَمُو دَغَ مَصَرْ؟ دُوانْمٜىٰ كَكَٰوُاْمُ أَنَنْ كَكَشٜىٰمُ دَ یَیَنْمُ دَ دَبُّواْبِنْمُ دَ ڧِشِنْ ضُوَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma jama'a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, “Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, domin ka kashe mu ne, da mu, da 'ya'yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?”