Exodus 17:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے ذَنْ ڟَيَ أَغَبَنْكُ أَوَنْثَنْ دُوڟٜىٰ كُسَدَ هُواْرٜىٰبْ؞ سَيْ كَبُغِ دُوڟٜىٰنْ، ضُوَ كُوَ ذَيْڢِتُواْ دَغَ ثِكِنْسَ دُواْمِنْ مُتَنٜىٰ سُشَا؞» أَغَبَنْ دَتَّاوَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، مُوسَٰى يَيِ أَبِنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.