Exodus 18:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Yetro surukin Musa, ya kawo hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu wa Allah, Haruna ya zo tare da dukan dattawan Isra’ila, suka ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يِتْرُواْ بَابَنْ مَاتَرْ مُوسَٰى يَمِيڧَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا دَ تَسَوْرَنْ هَدَايُ غَ اللَّهْ ؞ سَيْ هَٰرُونَ يَذُواْ تَرٜىٰدَ دُكَنْ دَتَّاوَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دُواْمِنْ سُثِ عَبِنْثِ تَرٜىٰ دَشِ أَغَبَنْ اللَّهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yetro, surukin Musa kuwa, ya miƙa hadaya ta ƙonawa da sadaka ga Allah. Sai Haruna ya zo tare da dattawan Isra'ila duka don su ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.