Exodus 18:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ بَابَنْ مَاتَرْ مُوسَٰى يَغَ دُكَنْ يَدَّ مُوسَٰى يَكٜىٰ ڢَامَ دُواْمِنْ جَمَعَرْ، سَيْيَثٜىٰ «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ وَنَّنْ دَ كَكٜىٰيِ وَجَمَعَ؟ دُوانْمٜىٰ كَكٜىٰيِنْ وَنَّنْ كَيْ كَطَيْ؟ دُوبِے يَدَّ مُتَنٜىٰ سُنَ أَڟَيٜىٰ كٜىٰوَيٜىٰ دَكَيْ تُنْدَغَ سَڢٜىٰ حَرْ ذُوَا يَمَّ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama'a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama'a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?”