Exodus 19:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya amsa, “Sauka ka kawo Haruna tare da kai. Amma kada firistoci da mutane su zarce iyakan nan, a kan za su zo wurin Ubangiji, don kada in hallaka su.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ مَسَ «تَاشِ كَسَوْكَ ڧَسَا، سَعَنً كَهَوْ تَرٜىٰدَ هَٰرُونَ؞ عَمَّا كَدَ كَبَرْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ جَمَعَ سُڧٜىٰتَرٜىٰ إِيَاكَرْ نَنْ دُواْمِنْ سُهَوْ وُرِينَ؞ إِنْ سُنْيِ حَكَ ذَنْ حُكُنْتَسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sauka, ka hau tare da Haruna. Amma kada ka bar firistoci da jama'a su ƙetare kan iyakar su hau zuwa wurina, don kada in hukunta su.”