Exodus 2:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً وَتَرَانَ سَعَدَّ مُوسَٰى يَيِ غِرْمَ، يَا تَڢِے وُرِنْ مُتَنٜىٰنْسَ، يَكُمَغَا يَدَّ سُكٜىٰ شَنْ وَهَلَ دَ عَيْكِنْ دُواْلٜىٰ؞ سَيْ يَغَ وَنِ مُتُمِنْ مَصَرْ يَنَ دُوكَنْ وَنِ دَغَ إِبْرَانِيَاوَا، طَيَ دَغَ ثِكِنْ یَنْعُوَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ana nan wata rana, sa'ad da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. Ya kuma ga wani Bamasare yana dūkan Ba'ibrane, ɗaya daga cikin 'yan'uwansa.