Exodus 2:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَشٜىٰغَرِ مُوسَٰى يَا سَاكٜىٰ ڢِتَ، سَيْ يَتَرَرْ دَ وَطَنْسُ إِبْرَانِيَاوَا بِيُ سُنَ ڢَطَ دَ جُونَ! يَثٜىٰ وَطَيَنْ دَ يَكٜىٰدَ لَيْڢِے «مٜىٰيَسَا كَكٜىٰ بُغُنْ طَنْعُوَنْكَ، طَيَ دَغَ مُتَنٜىٰنْكَ إِبْرَانِيَاوَا؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kashegari da ya sāke fita, sai ya ga waɗansu Ibraniyawa biyu suna faɗa da juna. Ya ce wa wanda yake ƙwaran ɗan'uwansa, “Me ya sa kake bugun ɗan'uwanka?”