Exodus 2:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَعَدَّ تَغَ بَذَاتَ عِيَ ڧَارَ ٻُواْيٜىٰشِ أَغِدَابَ، سَيْ تَسَاڧَ ݣُونْدُواْ نَثِيَوَرْ إِوَ، تَشَاڢٜىٰ ݣُونْدُوانْ دَ مَنْݣُولْتَ، دُواْمِنْ كَدَ يَنُڟٜىٰ عَثِكِنْ ضُوَ؞ سَيْ تَسَ جَرِرِنْ عَثِكِنْ ݣُونْدُوانْ، تَجٜىٰ تَأَجِيٜىٰ شِ عَثِكِنْ ثِيَوَ مَاسُ ڟَيِ عَبَاكِنْ كُواْغِنْ نِلُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu.