Exodus 20:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بَذَاكَيِ ݣُوطَيِنْ غِدَنْ مَڨُوبْثِنْكَبَ؞ بَذَاكَيِ ݣُوطَيِنْ مَاتَرْ مَڨُوبْثِنْكَ، كُواْ بَايِنْسَ مَظَا دَ مَاتَا، كُواْ شَانُنْسَ، كُواْ جَاكِنْسَ، كُواْ وَنِ أَبِنْدَ مَڨُوبْثِنْكَ يَكٜىٰ دَشِيبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”