Exodus 21:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“In bijimi ya kashe namiji ko ta mace, dole a jajjefe bijimin har yă mutu, ba za a kuma ci namansa ba. Amma mai bijimin ba shi da laifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ بِجِمِ يَسُواْكِ مَثٜىٰ كُواْ نَمِجِ حَرْ سُنْ مُتُ، دُواْلٜىٰنٜىٰ أَ جٜىٰجّٜىٰڢِ بِجِمِنْ دَ دُوَڟُو، بَذَاعَثِ نَامَنْسَبَ، بَذَاعَ كُمَ حُكُنْتَ مَيْ بِجِمِنْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Idan sa ya kashe ko mace ko namiji, to, lalle ne a jajjefi san da duwatsu, kada kuma a ci namansa, mai san kuwa zai kuɓuta.