Exodus 21:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In ba tă gamshi maigida wanda ya zaɓe ta domin kansa ba, dole yă bari a fanshe ta. Ba shi da dama yă sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ بَتَغَمْشِ مَيْغِدَنْتَ وَنْدَ يَسَيٜىٰتَ دَ نُڢِ تَذَمَ مَثٜىٰنْدَ يَأَجِيٜىٰبَ، سَيْ مَيْغِدَنْ يَبَرِ أَ ڢَنْشٜىٰتَ؞ عَمَّا مَيْغِدَنْتَ بَاشِ دَ یَنْثِ يَسَيَرْ دَ عِتَ غَ بَڧِبَ، تُنْدَيَكٜىٰ بَيْ ݣَوْتَا مَتَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan ba ta gamshi maigidanta wanda ya maishe ta kamar ɗaya daga cikin matansa ba, sai ya yarda a fanshe ta. Amma ba shi da iko ya sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.