Exodus 22:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kowane rikicin cin amana da zai shiga tsakanin mutum biyu, ko a kan bijimi, ko jaki, ko tunkiya, ko riga, kai, ko a kan kowane irin abin da ya ɓata, da ma abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin a gaban alƙalai. Wanda alƙali ya ce shi ne mai laifi, sai yă biya ɗayan taran da za a yanka, har sau biyu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ ضِكِثِ يَشِغَ ڟَكَانِنْ مُتُمْ بِيُ عَكَنْ وَنِ أَبِنْدَ بَعَتَبَّتَرْ دَ مَيْشِيبَ، كُواْ عَكَنْ بِجِمِ، كُواْ جَاكِ، كُواْ تُنْكِيَ، كُواْ رِغَا، كُواْ كُواْوَنٜىٰ أَبِنْدَ يَٻَتَ، سَيْ سُو بِيُ طِنْ سُذُواْ غَبَنْ اللَّهْ ؞ وَنْدَ اللَّهْ يَثٜىٰ شِينٜىٰ مَيْ لَيْڢِے، سَيْ يَمَيَرْوَ طَيَنْ حَرْ سَوْ بِيُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A kowane laifi na cin amana, ko sa ne, ko jaki, ko tunkiya, ko tufa, ko kowane ɓataccen abu, da abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin nan a gaban Allah. Wanda Allah ya ce shi ne da laifi, sai ya biya wa ɗayan ninki biyu.