Exodus 23:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا أَ شٜىٰكَرَا تَبَݣَويْ ذَاكَ بَرْ غُواْنَرْ تَهُوتَ بَذَاعَ نُواْمٜىٰ تَبَ، دُواْمِنْ مُتَنٜىٰنْكُ مَاسُ بُڧَاتَ سُثِ دَغَ أَمْڢَانِنْتَ؞ أَبِنْ دَ سُكَ بَرِ كُمَ، عَبَرْ نَمُواْمِنْ دَاجِ سُثِ؞ حَكَ ذَاكَيِ دَ غُواْنَرْكَ تَ إِنَبِے دَ تَظَيْتُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma a shekara ta bakwai, ku bar su su huta kurum, ba za ku girbi kome daga ciki ba, domin mutanenku matalauta su ci abin da ya ragu, namomin jeji kuma su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku na inabi da na zaitun.