Exodus 23:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاكَ عَيْكَتَ مُغُنْتَا سَبُواْدَ جَمَعَ مَڢِے يَوَ سُنَيِبَ؞ سَعَدَّ عَكَ كِرَاكَ دُواْمِنْ بَادَ شَيْدَ أَغَبَنْ شَرِيعَ، بَذَاكَ بَادَ شَيْدَرْ ڧَضْيَا دُواْمِنْ كَڢَرَنْتَ وَ جَمَعَ مَڢِے يَوَ رَيْ دُواْمِنْ أَ جُجُّويٜىٰ غَسْكِيَابَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari'a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci.